Babu shakka cewa a wannan zamanin ko kuma lokaci ba sai an nana-ta muhimmancin ilimi ba duba da irin yadda mutane da al'umma tai suke amfani da ilimiwurin ci da kan su da ma al'umar su gaba a duk fannoni na rayuwa kama daga kiwon lafiya, aikin gona, ƙere- ƙere, harma da tarbiya da sauransu. Duba da haka ne ya sa marigayi Halliru Aƙilu ke tambaya shin ko akwai wani namu ba ilimi ba? Babu tantama kamar yadda ya faɗa aikuwa babu domin ilimi ke sai ta rayuwr Ɗan Adam kuma ya bashi damar ɗora kansa adukkan matsayin da yake so a rayuwa.
Domin ganin an bawa kowanne ɗan Nigeria damar samun ilimi ingatacce wanda masu iya magana ke cewa "ilimi gishirin rayuwa" gwannatin Nigeria ta samar da makarantu a matakai daban-daban kama daga pramare, sakondare, da jami'a da dai sauransu.
National Open University of Nigeria jami'a ce ɗaya tilo tamkar da dubu wadda duk faɗin nahiyar Africa babu kamarta wadda aka kafata domin ta bawa yan Nigeria da ma wasun su ilimi a tsari na koyi daga inda kake, watu ayi karatu ba sai anzo aji kullumba ba kuma sai an zauna aguri ɗaya ba. Ɗalibi na iya yin karatun sa daga duk inda yake so domin ta na gunar da karatu ne harma da jarabawa ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa mai haɗe da yanar gizo gizo. Har ila yau a karƙashin wannan tsari ana bawa ɗalibai littattafai da za su dunga karantawa na tsawon lokaci kafin ayi jarabawar gwaji (test) da kuma jarabawar karshen zangon karatu wato (semester).
HaƘi ƙa, wannan Jami'a na dauke da tsarin karatu da zai bawa duk mai damuwa ta fuskar lokaci kamar masu aikin gwamnati, kampanoni, yan kasuwa, masu san'ar hannu misali ɗinki, kafinta, birkila, direba, mai fenti, magini, plumber, da dai sauransu. Daga cikin tsare tsaren sune ba a yin lacca, assignment da attendace kullum. Har ila yau jamiar na da shafi sukutum a yanar gizo da ke kunshe da dukkan littattafai da makaloli na fanni daban-daban domin amfanin dalibai. Tana kuma da sassa da yawa afadin Nigeria kamar Kano, Kaduna, Lagos Abuja duk dai domin a sauƙaƙawa mutane. Haka kuma an sauƙaƙa tsarin biyan kudin makaranta wato tuition fees ta yadda za abiya na zangon karatu maici ne Kawai kuma iyya na adadin darrusa (courses) da dalibi zai dauka a wannan zangon karatun zai biya kacal.
Duba da irin wannan tagomashi da wannan Jamia mai albarka ta ke dauke dashi dakuma yadda mutane ke rasa gurbin karatu a sauran jami'oin kasarnan da Kuma matukar alfanun da wanna jami'ar take dashi musamma ga masu zaman kansu ko sana'ar hannu tasa a mai-maita janhakali anan. Ya kamata mai san'ar hannu kamar kafinta, birkila, direba, mai fennti, mai tuya kosai da sauran Su agida da bakin titi, mai sai da ruwa akura, mai tireda da dai sauransu su fahimci duniya ta chanza ayau komai zamanan tar dashi ake yi kuma jagoran zamani shine ilimi. Da ilimi za su iya bunƙasa sana'arsu fiye da duk yadda suke zato. Ilimi zai basu damar yin mu'amala ta zamani, cinikin zamani, hanyoyin Ƙawata kayan su da hajojun su na zamani domin bunkasa ciniki da riba.
Ya kamata lallai su fahimci cewa karatu a National open University of Nigeria da mace da babu irinta domin za su inganta rayuwarsu, su bunƙasa kasuwancin su da sana'ar su batare da fuskantar ƙalubale na lokaci, na ƙa'idojin shiga jami'a (admission requirements) ko kudi ba domin dukka wadannan matsaloli an kauda su a wannan jami'a mai albarka. Saura da me Ku tuntubi jami'a domin Neman burn n karatu ko Karin bayani awanna Shafin yanar gizo www.nounonline.com. National Open University of Nigeria ingatacciya ce kamar kowacce jami'a a Duniya.